in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mahukuntan kasar Sin sun ayyana kudurin kara samar da kudade domin yaki da talauci
2016-10-17 11:11:46 cri
Mahukuntan kasar Sin sun fidda wata takardar bayanai a hukunce, wadda ke kunshe da kudurin samar da karin kudade, domin yaki da talauci cikin shekaru 5 masu zuwa.

Takardar wadda aka fitar a Litinin din nan, ta bayyana cewa gwamnati za ta shigar da kudade masu yawa ga yankunan da suka fi fama da talauci domin dakile fatara, da samar da ci gaba mai dorewa.

Takardar mai lakabin "Ci gaban Sin a fannin yaki da fatara da kare hakkin bil'adama", ta nuna cewa, kudin da aka tanada domin wannan aiki, za su kai kudin kasar Sin RMB biliyan 189.84, kimanin dalar Amurka biliyan 28.17. Za kuma a kashe su ne tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015.

Ya zuwa karshen shekarar bara, Sin na da yawan matalauta da suka kai mutane miliyan 55.75, wadanda kuma ake fatan fitar da su daga wannan yanayi nan da shekara ta 2020.

Cikin shekaru 30 da suka gabata, tun fara aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje, da sauye sauye ga tattalin arzikin kasa, mahukuntan kasar sun cimma nasarar ceto kimanin mutane miliyan 700 daga kangin talauci.

Rahoton MDD game da kudurorin ci gaban karni na bara, ya nuna cewa adadin wadanda ke cikin matsanancin kangin talauci a kasar Sin ya sauya, daga kaso 61 bisa dari a shekarar 1990 zuwa kaso 4.2 a shekarar 2014. A hannu guda kuma kaso na matalauta da kasar ta ceto daga wannan yanayi, ya kai kaso 70 bisa dari na jimillar adadin a dukkanin fadin duniya. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China