Mamban kwamitin kula da harkokin kasa da kasa na majalisar Duma ta kasar Sergei Zheleznyak ya ce, "ko shakka babu yaki da ta'addanci aiki ne da ya fi muhimmanci a gaban kasashen Rasha da Sin, yarjejeniyar din ta aza harsashi ga hadin kai a tsakanin kasashen biyu wajen yaki da ta'addanci ta fuskar dokoki."
An cimma wannan yarjejeniya ne a ranar 27 ga watan Satumba na shekarar 2010 a birnin Beijing. (Bilkisu)