Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya yi kira da a kara kwazo wajen yaki da ayyukan ta'addanci ta yanar gizo, domin a cewar sa hakan zai bada damar dakile hanyoyin da 'yan ta'adda ke bi wajen yada munanan akidun su.
Mr. Liu Jieyi ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, yayin taron kwamitin tsaron MDD game batun hadin gwiwar tsaro tsakanin MDDr da kungiyar kasashen musulmi ta OIC.
Liu ya kara da cewa kamata yayi gamayyar kasa da kasa su fadada kokari, wajen sa ido kan yanar gizo, duba da yadda masu tada kayar baya ke amfani da wannan kafa waje tattara kudade, da tsara hare haren ta'addanci.
Ya ce ta'addanci na zama wata barazana ga kasashen duniya, don haka yaki da shi ya zama wani muhimmin aiki da MDD tare da kungiyar OIC ya kamata su baiwa kulawa.
Kaza lika Mr. Liu ya bayyana bukatar tattaunawa tsakanin sassa daban daban, domin cimma nasarar samar da daidaito da hadin kai, tare da tabbatar da adalci tsakanin al'ummun duniya.(Saminu Alhassan)