in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu bambanci kan aikin yaki da ta'addanci, in ji shugaban Rasha
2016-08-06 13:01:39 cri
Jiya Jumma'a 5 ga wata, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bayyana a yayin dake zantawa da kafofin watsa labarai cewa, ya kamata bangarori daban daban su hada kai wajen yaki da dukkan iri ta'addanci, bai kamata a nuna bambanci kan wannan aiki ko kadan ba.

Mr. Putin ya bayyana haka ne kafin ziyarar da zai kai a kasar Azerbaijan. Haka kuma, an ce, a ran 8 ga wata, za a yi taron shugabannin kasashen Rasha, Azerbaijan da kuma Iran karo na farko a babban birnin kasar Azerbaijan, Baku.

Bugu da kari, shugaba Putin ya jaddada cewa, kwanan baya, an yi ta kai hare-haren ta'addanci a wurare daban daban na duniya, lamarin da ya nuna mana cewa, hadin gwiwar kasa da kasa kan yaki da ta'addanci ita ce hanyar kadai da za a iya cimma nasarar yaki da ta'addanci, kana, bisa dokokin kasa da kasa, ya kamata MDD ta dauki nauyinta na aikin shiga tsakani yadda ya kamata domin taimakawa kasa da kasa kan wannan aiki.

Kaza lika, ya ce, bai kamata a nuna bambanci kan aikin yaki da ta'addanci ba, sabo da dukkan 'yan ta'adda sun zama iri daya, ba wanda ya fi mugunta, ko wanda ya fi tausayi, haka kuma, ba za a amince da duk wanda yake son cimma moriyar siyasa ta hanyar yin amfani da 'yan ta'adda da kuma masu tsattsauran ra'ayi ba, sabo da haka zai kasance hadari mai tsanani ga kasa da kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China