A jiya Talata, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Liu Jieyi, ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakan yaki da cin zarafin kananan yara wanda kungiyoyin 'yan ta'adda ke yi, sannan ya kamata a kawar da mummunan tasiri da ra'ayin ta'addanci ke haifarwa ga yara kanana.
Liu Jieyi ya yi jawabi a gun taron muhawara na "yara da rikici" na kwamitin sulhu na MDD inda ya bayyana cewa, rikice-rikice suna haddasa cin zarafin yara a wasu kasashen duniya. A sakamakon yawaitar kungiyoyin 'yan ta'adda, ana kara samun rahotannin hallaka yara da kuma yin amfani da su wajen gudanar da ayyukan ta'addanci. Ya kamata kasashen duniya su dauki kwararan matakai domin hana kungiyoyin 'yan ta'adda shigar da kananan yara harkar ta'addanci ta hanyar amfani da yanar gizo. Kana ya kamata a kara ba da ilmi ga yara domin kawar da ra'ayoyin ta'addanci a gare su. (Lami)