in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya ba da jawabi a yayin taron APEC
2016-11-20 13:36:52 cri
Jiya Asabar 19 ga wata da safe, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron shugabannin dake kula da harkokin masana'antu da kasuwanci na kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC da aka yi a birnin Lima na kasar Peru, inda ya kuma ba da wani jawabi mai taken "zurfafa dangantakar abokantaka dake tsakaninmu da kuma karfafa kwarewarmu wajen neman bunkasuwa".

Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya ba da shawarwari guda hudu ta fuskar yadda za a warware kalubalolin dake gabanmu wajen raya yankin Asiya da Pasifik, kuma wadannan shawarwari sun hada da, na farko, ya kamata a inganta dunkulewar tattalin arizki yadda ya kamata domin raya tattalin arzikin duniya cikin budewar kofa, sa'an nan kuma, ya kamata a karfafa hadin gwiwa da mu'amalar dake tsakanin kasa da kasa, domin cimma burinmu na neman bunkasuwa cikin hadin gwiwa, na uku kuma, ya kamata a ci gaba da sabunta shirye-shiryen raya tattalin arziki bisa halin da ake ciki yadda ya kamata, ta yadda za a karfafa karfinmu wajen neman bunkasuwa, a karshe dai, ya kamata a ciyar da hadin gwiwarmu gaba domin cimma moriyar juna, da kuma zurfafa dangantakar abokantaka dake tsakanin bangarori daban daban da abin ya shafa bisa manyan tsare-tsare.

Haka kuma, Xi Jinping ya jaddada aniyar kasar Sin wajen kara bude kofa ga waje, ya ce, kasar Sin za ta aiwatar da manufofin kara bude kofa ga waje cikin himma da kwazo, inda za ta kyautata ayyukan da abin ya shafa bisa fannoni daban daban kuma yadda ya kamata. Sa'an nan, kasar Sin za ta ba da karin damammaki ga 'yan kasuwa na ketare da su shiga kasar Sin, ta yadda za ta karfafa ayyukanta wajen gina yankin ciniki cikin 'yanci, yayin da take kyautata dokoki da ayyukan da abin ya shafa kan wannan aiki, da kuma nuna adalci ga bangarori daban daban dake shafar harkar kasuwanci a kasar Sin.

Bugu da kari, shugaba Xi ya nuna imani cewa, kasar Sin za ta ci gaba da samar wa kamfanonin kasashen ketare damammaki na neman bunkasuwa cikin adalci kuma ba tare da boye kome ba a cikin kasar, bisa matakan da kasar ta dauka wajen kyautata manufofin da abin ya shafa.

A karshe, Xi Jinping ya jaddada cewa, kasar Sin ta tsayawa tsayin daka wajen neman ci gaban kasa cikin zaman lafiya, da kuma aiwatar da manufar neman bunkasuwa ta cimma moriyar juna, shi ya sa, za ta ci gaba da ba da gudummawa wajen raya kasashen dake yankin Asiya da Pasifik a lokacin da take neman bunkasuwar ita kanta, da kuma samar wa al'ummomin yankin karin tallafi da damammaki yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China