A yau Jumma'a ne, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya aika wa Ban Ki-moon, babban magatakardan MDD wasikar murna dangane da yadda yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris ta fara aiki a hukumance.
A cikin wasikarsa, shugaba Xi ya ce, yarjejeniyar Paris ta bude wani sabon babi kan yadda za a magance sauyin yanayi cikin hadin gwiwar kasa da kasa. Kasar Sin tana cike da imanin cewa, nan ba da dadewa ba aikin tinkarar sauyin yanayi zai yi nasara, kasar Sin tana son inganta cudanya da hadin gwiwa da sassa daban daban, ta yadda za ta ba da gudummawa a kokarin da kasashen duniya ke yi na bullo da tsarin daidaita sauyin yanayi bisa adalci. (Tasallah Yuan)