in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya isa Lima don halarci kwarya-kwaryar taron koli na APEC da kuma kai ziyara a Peru
2016-11-19 13:25:12 cri

Jiya Juma'a, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isa Lima, don halartar kwarya-kwaryar taron koli karo na 24 na kungiyar APEC, tare kuma da kai ziyarar aiki a jamhuriyar Peru.

A yayin bikin da aka shirya don maraba da shi a filin jirgin saman kasar, shugaba Xi, ya nuna sahihiyar gaisuwa da fatan alheri ga jama'ar kasar Peru. Kana ya ce, kasar Peru muhimmiyar kasa ce dake Latin Amurka. A cikin shekaru 45 da suka gabata da aka kulla huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Peru, kullum kasashen biyu na tsayawa kan manufofin zaman daidai wa daida ne, da samun moriyar juna, da kuma nuna girmamawa ga juna. A yanzu haka, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na samun cigaba yadda ya kamata, kuma suna da makoma mai kyau wajen hadin kai a nan gaba.

Xi ya kara da cewa, ya kawo ziyarar ne da nufin karfafa zumunci, da habaka ra'ayin bai daya, da zurfafa hadin kai da kuma neman cigaba a tsakanin kasashen biyu. Yana mai cewa, kasar Sin tana goyon bayan kasar ta Peru wajen shirya kwarya-kwaryar taron koli karo na 24 na kungiyar APEC. Xi ya ce, yana sa ran yin musayar ra'ayoyi tare da shugabannin Peru kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da kuma wasu batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake jawo hankulansu duka.

Shugaba Xi ya isa kasar Peru ne bayan ziyararsa a kasar Ecuador, daga baya kuma zai kai ziyara a kasar Chile. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China