in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halartar taron APEC da shugaba Xi zai yi za ta ingiza dinkewar tattalin arzikin yankunan Asiya da Fasifik
2016-11-10 19:59:25 cri
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong, ya bayyana halartar taron kolin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin yankunan Asiya da Fasifik wato APEC da shugaban kasar Sin zai yi, a matsayin wani mataki na kara hade tattalin arzikin yankunan waje guda.

Mr. Li ya ce shugaba Xi zai halarci taron kungiyar ta APEC dake tafe a birnin Lima na kasar Peru, tsakanin ranekun 19 zuwa 20 ga watan nan na Nuwamba, taron da aka yiwa take da "ci gaba mai nagarta da alakar sa da bunkasar rayuwar bil Adama.

Ya ce niyyar shugaba Xi ta halartar wannan taro, na dada tabbatar da muhimmanci da kasar Sin ke nunawa, ga hadin gwiwar yankunan na Asiya da Fasifik.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China