in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasashen Sin da Ecuador sun halarci wasu bukukuwa
2016-11-19 13:33:35 cri
A Jiya Juma'a shugaban kasar Sin da takwaransa na kasar Ecuador Rafael Correa Delgado, sun halarci bikin bude dakin gwaji na cibiyar ba da jagoranci kan tsaron jama'a ta gaggawa na Ecuador a Quito, wanda kasar Sin ce ta bada tallafin kafa shi. Baya ga haka, sun halarci bikin aza harsashi na asibitin Chone, kuma ta hanyar bidiyo ne suka halarci bikin kammala aikin tashar samar da wutar lantarki ta ruwa.

A yayin jawabinsa, shugaba Xi ya nuna cewa, kasashen Sin da Ecuador suna da zumunta mai dogon tarihi. A shekarun nan, kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu cigaba a dukkan fannoni, kana an daga matsayin dangantakar zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. Kasar Sin na fatan zurfafa hadin kai tare da Ecuador, don ciyar da dangantakar dake tsakaninsu gaba.

A nasa bangaren, shugaba Correa, ya bayyana cewa, hadin kai a tsakanin bangarorin biyu ya taimakawa kasarsa wajen kyautata manyan kayayyakin more rayuwa, da inganta makamashi maras gurbata muhalli, da kuma kyautata ayyukan tsaron jama'a. Kasarsa ta yi godiya ga irin goyon bayan da Sin ta bayar a fannonin sake raya kasa bayan bala'in da kasar ta fuskanta, da bunkasuwar kasa, kana kasarsa ma tana fatan karfafa hadin kai irin na samun cin moriyar juna a tsakanin kasashen biyu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China