in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya gana da Vladimir Putin
2016-11-20 12:53:42 cri
Jiya Asabar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a birnin Lima na kasar Peru.

A yayin ganawar tasu, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kamata kasar Sin da kasar Rasha su kara zurfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa tsarin kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, da kuma aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa da aka kulla a yayin taron Beijing da dai sauran tarukan da aka yi a 'yan shekarun nan yadda ya kamata, domin ciyar da yunkurin yankin ciniki cikin 'yanci a yankin Asiya da Pasifik gaba, da kuma cimma nasarar gudanar da taron da ake yi a birnin Lima a halin yanzu, ta yadda kungiyar APEC za ta iya ba da karin gudummawa ga bunkasuwar tattalin arziki a yankin Asiya da Pasifik, har ma a duk fadin duniya baki daya.

A nasa bangare kuma, shugaba Putin ya ce, kasar Rasha tana sa ran cigaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin domin inganta ayyukan raya kawancen tattalin arziki na yankin Turai da Asiya, yayin da ake karfafa ayyukan raya shirin zirin tattalin arziki na hanyar siliki ta ruwa na karni na 21, shi ya sa, ya kamata kasar Sin da kasar Rasha su habaka hadin gwiwar dake tsakaninsu bisa fannoni daban daban da suka hada da batun kungiyar APEC da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China