Xie Zhenhua, manzon musamman na kasar Sin mai kula da sauyin yanayi ya bayyana cewa, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen magance matsalar sauyin yanayi, baya ga nasarar cimma manufarta a wasu fannoni da aka tanada cikin shirinta na raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 12 kafin lokacin da ta tsara. Mista Xie ya fadi haka ne yau Talata 1 ga watan Nuwamba a nan Beijing.
Dangane da taron Marrakech da za a bude nan ba da dadewa ba, mista Xie ya ce, kasar Sin tana sa ran cewa, taron zai ba da damar aiwatar da matakan da aka tanada a yarjejeniyar Paris.
A ranar 7 zuwa 18 ga wata ne aka sa ran bude babban taron kasashen da suka sa hannu kan yarjejeniyar MDD kan sauyin yanayi karo na 22 a birnin Marrakech na kasar Morroco. Kuma wannan shi ne karo na farko da aka gudanar da irin wannan babban taro tun bayan da yarjejeniyar ta fara aiki. (Tasallah Yuan)