in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kafa asusun yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe maso tasowa dangane da sauyin yanayi
2015-06-27 13:13:14 cri
A yau Asabar 27 ga wata a nan birnin Beijing, Zhang Yong, mataimakin darektan kwamitin yin gyare-gyare da raya kasar Sin ya bayyana cewa, kasar na dora muhimmanci sosai kan yin hadin gwiwa da kasashen duniya wajen daidaita sauyin yanayi. Tun daga shekarar 2011 har zuwa yanzu, kasar Sin kan kebe dalar Amurka fiye da miliyan 10 a ko wace shekara domin taimakawa da kuma goyon bayan sauran kasashe masu tasowa wajen kyautata kwarewar daidaita sauyin yanayi, musamman ma kasashen da ke kan kananan tsibirai, kasashe mafiya rashin ci gaba da kasashen Afirka. Mr. Zhang ya ce a nan gaba kasar Sin za ta rubanya kokarinta wajen kara azama kan hada kai a tsakanin kasashe maso tasowa, tare da kafa wani asusun yin hadin gwiwa a tsakaninsu kan daidaita sauyin yanayi.

Mista Zhang ya fadi haka ne a yayin taron koli na fitattun mashawarta na kasa da kasa karo na 4 da aka yi a wannan rana yana mai cewa, yanzu kasar Sin na yin nazari da kuma tsara manufar daidaita sauyin yanayi daga shekarar 2016 zuwa 2020. Za ta kuma kara kyautata manufofi da matakai nagartattu bisa tanade-tanaden da ke cikin manyan tsare-tsaren kasar dangane da daidaita sauyin yanayi.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China