Bugu da kari, Xi Jinping ya ce, ta'addanci ya kasance wani babban kalubale dake gaban al'ummomin kasa da kasa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen yaki da dukkan nau'o'in ta'addanci, tana kuma goyon bayan kasar Faransa wajen kiyaye tsaron kasarta, shi ya sa, kasar Sin tana son karfafa hadin gwiwa tare da kasar Faransa a wannan fanni, domin kiyaye tsaron kasashen biyu, da na kasashen duniya baki daya. (Maryam)