in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Boko Haram babban kalubale ne ga ci gaban tattalin arzikin Afrika, in ji shugaban Benin
2015-06-10 10:24:55 cri

Matsalar Boko Haram ta kasance wani babban kalubale ga ci gaban tattalin arzikin kasashen da ke shiyyar da suka hada da Nijar, Kamaru da Chadi wadanda suka shiga yaki da wannan kungiyar ta'addanci ta Najeriya, a cewar shugaban kasar Benin Boni Yayi, bayan ganawarsa a ranar Talatar da ta gabata tare da shugaban kasar Faransa Francois Hollande.

Kasashe kamar su Kamaru, Chadi da Nijar sun yi kokari sosai wajen zuba makudan kudade da farko aka kebe domin biyan bukatun al'ummominsu, amma aka jiya akalarsu domin fuskantar wannan matsala. Boko Haram ta zama babban kalubale dake janyo kashin kudaden da aka kebe ga bunkasuwar wadannan kasashe, in ji shugaba Boni Yayi a gaban manema labarai, bayan ganawarsa tare da takwaransa na Faransa.

Shugaban kasar Benin, ya sanar da shirya wani taron shugabannin kasashen Nijeriya, Nijar, Chadi, Kamaru da Benin a ranar 11 ga watan Yuni a birnin Abuja domin tsai da matakan yaki da Boko Haram.

A ganinsa, hada karfi da karfe shi ne muhimmin matakin kawo karshen wannan kungiyar ta'addanci domin idan babu tsaro, to ba za'a samun zaman lafiya ba.

Kasashen Nijar, Chadi, Kamaru, Benin da Nijeriya sun dauki wannan yunkuri domin nuna ci gaban tattalin arziki mai karfi dake cike burin ciyar, suturta, kulawa da lafiya da samar da aikin yi ga matasa. Amma Boko Haram ta zo yi wa wannan muhimmin yunkuri kafar angulu, in ji Boni Yayi.

Game da kasarsa da ta sanar da tura sojojinta a cikin rundunar hadin gwiwa domin yaki da Boko Haram, shugaba Boni Yayi ya tabbatar da cewa, sojojin Benin a shirye suke.

Haka kuma, mista Boni Yayi ya bayyana imaninsa na samun nasara kan yaki da 'yan ta'addan Najeriya, domin sabon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ya gana da shi bayan zabensa, ya dauki matsalar da muhimmanci. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China