Ma'aikatar tsaron kasar Faransa ta bayyana cewa, mayakanta sun yi nasarar kashe jiga-jigan mayakan 'yan tawayen kungiyoyin Al-Qaeda da ke yankin Maghreb (AQIM) da kuma Ansar Eddine a arewacin kasar Mali.
Wata sanarwa da ma'aikatar ta sanya a shafinta na Internet ta ce, dakarunta sun yi nasarar kashe Amada Ag Hama wanda aka fi sani da Abdelkarim the Touareg, da Ibrahim Ag Inawalen wanda aka fi sani da Bana a yayin wani farmakin da suka kaddamar da dare.
Ma'aikatar ta kara cewa, an kuma hallaka wasu 'yan tawayen biyu a lokacin wannan fafatawa, sai dai ba ta yi wani karin haske game da asalinsu ba.
Ana zargin kungiyoyin 'yan tawayen biyu da kai hare-haren ta'addanci kan dakarun kasa da kasa, tare da tayar da hankulan fararen hula a Mali. (Ibrahim)