in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka da Faransa sun sha alwashin karfafa hadin kai domin yakar IS
2015-07-07 10:12:15 cri

Sakataren harkokin tsaron kasar Amurka Ash Carter a ranar Litinin din nan ya gana da ministan tsaron kasar Faransa Jean-Yves Le Drian a ofishin sa dake Pentagon na Amurka, inda ya yi alkawarin ci gaba da hadin gwiwwa tsakanin kasashen 2 domin yakar kungiyar 'yan ta'adda ta IS.

Jami'an biyu sun kuma gana da manema labarai tare bayan tattaunarwar su wadda ta mai da hankali a kan kokarin da suke na yaki da kungiyar IS.

A lokacin ganawar, Mr Carter ya yaba wa kasar Faransa bisa ga kokarin ta a wannan aiki domin samar da sakamakon karshe dawwamamme na murkushe kungiyar IS, wani aiki da kasashen biyu duka suka amince yana bukatar lokaci mai tsawo da ba sassautawa.

A nashi bangaren, Jean-Yves Le Drian ya ce, kungiyar IS ta tashi daga kungiyar 'yan ta'adda, ta koma rundunar soji ta 'yan ta'adda. Wannan sauyin na nufin dole ne a yaki da IS daga dukkan bangarori. Ya ce, yanzu IS tana da karfin aiki kamar duk wata cikakkiyar rundunar soji ta zamani da kuma ta wajen gudanar da ayyukan ta a birane da sauran ayyuka na ta'addanci, abubuwa 3 da duk take iya aiwatarwa.

Ministan na kasar Faransa sai dai kuma ya kare aniyar hadin gwiwwa da za'a yi a kan kungiyar, wanda ya ce, maimaita harin da suke kai wa Iraqi ya ba su damar daidaituwa, ba wai don su yi nasara ba, sai don su daidaita yanayin da ake ciki, aikin da ya zama mai daukan lokaci.

A cewar sanarwa daga hukumar tsaron Amurkan ta Pentagon, jami'an tsaron kasashen biyu sun kuma tattauna yadda za su inganta ayyukan musanyar bayanan sirri tsakanin sojojin kasashen biyu domin dakile aiwatar da duk wani aikin ta'addancin. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China