A ranar Alhamis da yamma, wata motar daukan kaya ta kutsa kai cikin taron jama'a dake kallon wasan wuta a albarkacin bikin kasa a birnin Nice dake kudancin Faransa, lamarin da ya janyo a kalla mutuwar mutane 77, da jikkata wasu fiye da 50.
Motar ta kutsa kai cikin jama'a a lambun shan iska na "promenade des Anglais", bayan wasan wuta, tare da hallaka a kalla mutane 77, in ji Christan Estrosi, shugaban yankin Provence-Alpes-cote-d'Azur, a lokacin da yake hira da kafar BFMTV.
A cewarsa, akwai makamai da nakiyoyi cikin motar, kuma 'yan sanda sun harbe direban, tare da tabbatar da cewa, mutumin ya yi harbi cikin taron jama'a.
A cewar ministan cikin gida, ba a yi garkuwa da mutane ba, kuma babu wani mutumin da ya ja daga a wani wuri, kuma kwamitin ministoci kan halin ko ta kwana ya fara aiki.
Kotun yaki da ta'addanci ta birnin Paris ta bude bincike kan laifin kisa da yunkurin kisa tare da alaka da wata kungiyar ta'addanci.
Ofishin magajin garin Alphes-Maritimes ya yi maganar wani hari tare da yin kira ga jama'a da su tsaya gidajensu, a cewar kafofin yada labarun wuraren. (Maman Ada)