Haka zalika, ya ce, a halin yanzu, kasar Sin ta shiga lokacin da ake fi samun bala'un ambaliyar ruwa da kuma mahaukaciyar guguwa, ya kamata a mai da hankali sosai domin yin rigakafi kan hadarorin da mai iyuwa ne za su tashi sakamakon wadannan bala'u, ta yadda za a iya tabbatar da tsaron jama'ar kasa yadda ya kamata.
Bugu da kari, ya ce, ya kamata a ci gaba da karfafa ayyukanmu na fuskantar da harkokin gaggawa, yayin da kuma kara yin bincike a wuraren madatsun ruwa da aka gina ta da duwatsu, matarin ruwa da kuma tashoshin samar da wutar lantarki ta karfin ruwa da dai sauransu, domin kawar da kalubalen tsaro cikin lokaci. Sa'an nan kuma, ya kamata a gaggauta ayyukan yin rigakafi kan ambaliyar ruwa da kuma fitar da ruwan dake shiga birane, a sa'i daya kuma, a kyautata shirin kwashe mutanen dake fama da bala'i zuwa wurare na daban da kuma shirin fuskantar da harkokin gaggawa a wuraren da bala'in ya shafa da dai sauransu, domin yin shiri kan yaki da bala'in ambaliyar ruwa da dai sauran bala'un da suka shafi kasa wadanda mai iyuwa ne za su tashi sakamakon ambaliyar ruwa. (Maryam)