in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe da dama sun gudanar da bikin tunawa da ranar cika shekaru 10 da abkuwar bala'in tsunami
2014-12-27 17:32:47 cri
A jiya Asabar ne aka cika shekaru 10 da aukuwar bala'in murdawar babbar igiyar ruwa ta tsunami, inda kasashe da dama suka gudanar da tarukan tunawa da aukuwar wannan bala'in, da nuna jimami game da rasuwar dubban jama'a sakamakon aukuwar annobar.

An dai gudanar da gaggarumin bikin tunawa da wannan rana a birnin Banda Aceh, hedkwatar yankin musamman na Aceh dake kasar Indonesiya, inda mataimakin shugaban kasar, Yusuf Kalla ya yi jawabin godiya, ga al'ummun gida da na waje, wadanda suka shiga ayyukan ceto, da na farfadowar kasar bayan abkuwar bala'in.

A daren jiyan kuma, an gudanar da wani bikin na daban, a jihar Phang Nga dake kudancin Thailand, inda firaministan kasar, Prayuth Chan-ocha ya bayyana cewa, yanzu haka an riga an kafa tsarin kiyasta yiwuwar abkuwar ambaliyar ruwa ta tsunami, da tsarin ceto na zamani a kasar, matakin da ya baiwa kasar karfi, na kare kai, da ma rayukan baki masu shiga kasar daga wannan bala'i.

A Sri Lanka kuma, dubban jama'ar kasar sun yi wani gangami na musamman, tare da yin shiru na tsawon mintoci uku, domin nuna alhini ga wadanda suka rasu, su sama da dubu 40 a ya yin bala'in, tare da fatan alheri ga kasar.

A ranar 26 ga watan Disambar shekarar 2004 ne aka samu aukuwar girgizar kasa mai tsanani a yankin teku dake kusa da tsibirin Sumatra na Indonesiya, wadda ta haddasa murdawar igiyar ruwa ta tsunami, da ba a ga irin ta ba a shekaru 100 da suka wuce a tekun Indiya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China