in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya ba da umurnin ba da ceto game da abkuwar bala'in mahaukaciyar guguwa a lardin Jiangsu
2016-06-24 09:30:57 cri

A jiya Alhamis 23 ga wata da karfe 2 da yamma, wata mahaukaciyar guguwa ta afkawa wasu yankunan dake garin Funing da Sheyang na birnin Yancheng na larding Jiangsu, tare da lalata gine-gine da makarantu da kuma wasu hanyoyin motoci. Ya zuwa karfe 9 da rabi da yamma na ranar 23 ga wata, mutane 78 suka mutu yayin da mutane kimamin 500 suka ji rauni a sakamakon bala'in.

Bayan abkuwar bala'in, shugaban kasar Sin Xi Jinping dake ziyara a kasar Uzbekistan tare da halartar taron koli na SCO ya ba da umurni cewa, majalisar gudanarwar kasar Sin ta tura rukunin aiki zuwa yankin don ba da jagoranci ga aikin ceto, tare da jajantawa jama'ar dake fama da bala'in a madadin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin da majalisar gudanarwar kasar. Kana ya bukaci da a nuna kulawa sosai ga mutanen da suka ji rauni, da magance karuwar yawan mutanen da suka mutu ko raunata, tare da tsugunar da jama'ar dake fama da bala'in. Hakazalika kuma, ya bukaci hukumomin da abin ya shafa da su kara gudanar da aikin hasashen yanayi da binciken bala'i, da kuma rigakafin bala'i mai tsanani da tsugunar da mutanen dake fama da bala'i, da kuma tabbatar da tsaron jama'a da dukiyoyinsu.

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya ba da umurni cewa, a yi kokarin ba da ceto ga mutanen dake fama da bala'in, da yin bincike kan yanayin bala'in, da taimakawa mutanen farfado da zaman rayuwarsu cikin hanzari.

Bisa bukatun shugaba Xi Jinping da firaminista Li Keqiang, ma'aikatar harkokin jama'ar kasar da hukumomin da abin ya shafa sun riga sun tura rukunin aiki zuwa yankin. A halin yanzu, ana gudanar da aikin ba da ceto a wuraren yadda ya kamata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China