in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ambaliyar ruwa a wurare da dama dake kudancin kasar Sin
2016-06-28 11:04:50 cri
A kwanakin baya, an samu ruwan sama mai tsanani a kudancin kasar Sin, lamarin ya haddasa ambaliyar ruwa mai tsanani a Chongqing, Guizhou, Sichuan da sauran wuraren kasar.

A gun taron yaki da bala'in ambaliyar ruwa a birnin Chongqing da aka gudanar a ranar 27 ga wata, an ce, bayan da aka shiga yanayin ambaliyar ruwa, yawan ruwan saman da aka samu a birnin Chongqing ya karu da kashi 30 cikin dari bisa na makamancin lokaci na shekarun baya, ya zuwa yanzu mutane fiye da miliyan 1 da dubu 400 na yankuna da garuruwa 31 suna fama da bala'in, kuma mutane 19 sun mutu a sakamakon bala'in.

Hukumar harkokin jama'a ta lardin Guizhou ta bayyana cewa, ruwan saman da aka samu ya lalata amfanin gona da muraba'insu ya kai eka fiye da 2600. Kana an samu lalacewar hanyoyin mota da dama tare da gidajen jama'a da dama a garin Nayong a sakamakon gangarowar duwatsu da laka domin ruwan saman da aka samu. Yanzu gwamnatin wurin tana gudanar da ayyukan ba da ceto da yaki da bala'in cikin sauri.

A lardin Sichuan, mutum daya ya mutu a sakamakon bala'in a birnin Dazhou dake lardin, kuma an lalata hanyoyin motoci da dama, an yi hasashen cewa, bala'in zai haddasa hasarori da kudin Sin Yuan miliyan 5.3. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China