Li Keqiang ya ce, watan Yuli da watan Agusta su ne muhimmin lokacin gudanar da aikin yin rigakafi kan ambaliyar ruwa, ya kamata a mai da hankali sosai kan ayyukan yin rigakafi da yaki da ambaliyar ruwa, haka kuma ya bukaci hukumonin da abin ya shafa su yi hadin gwiwa yadda ya kamata domin gudanar da ayyukan gaggawa, yayin aiwatar da aikin yaki da ambaliyar ruwa da aikin ceto yadda ya kamata.
Kaza lika ya ce, tsaron madatsar ruwa da aka gina ta da duwatsu da kuma tsaron matarin ruwa suna da muhimmanci wajen yin rigakafi kan ambaliyar ruwa, ya kamata a gudanar da bincike a wurare cikin lokaci, yayin da yin aikin shiryawa bisa yanayin da ake ciki yadda ya kamata, ta yadda za a tabbatar da tsaron yankin.
Bugu da kari, ya ce, ya kamata a karfafa aikin bincike da yin rigakafi kan hadari a yankunan da bala'in ya shafa domin kiyaye tsaron al'ummomin kasar, kana ya kamata hukumar kudi ta gwamnatin kasar ta gaggauta samar da kudaden yin rigakafi da yaki da ambaliyar ruwa ga wuraren da bala'in ya shafa, da kuma ba da jagoranci kan ayyukan samar da bayanan gargadi, da shirya kayayyakin agaji, da tura ma'aikata zuwa wurare da dai sauransu ta yadda za a iya cimma nasarar yaki da wannan bala'i na bana cikin hadin gwiwa. (Maryam)