Tashar yanar gizo ta ma'aikatar harkokin cikin gida na kasar Sin ta sanar a ranar talatan nan 22 ga wata cewa, mahaukaciyar guguwa mai lamba 9 da ake kira "Rammasun" ta ratsa larduna Guangdong, Guangxi, Hainan, Yunnan da dai sauran yankunan kasar Sin, lamarin da ya sanya wuraren ke fuskantar ruwan sama mai karfi daya janyo ambaliyar ruwa, kankara, zaizayar kasa da dai sauran bala'u, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 46 yayin da wasu 25 suka bace.
Rukunin musamman mai kula da aikin tinkarar bala'in na gwamnatin jihar Yunnan ya bayyana cewa, wasu hukumomi suna iyakacin kokarin ceton mutane da samar da jiyya ga wadanda suka ji rauni da kaurad da mutanen da bala'in ya ritsa da su, da kuma tabbatar da ingancin zaman rayuwarsu da dai sauran ragowar ayyukan ceto da ya kamata. (Amina)