in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi gargadin yiwuwar fuskantar ruwan sama mai tsanani a lardin Hunan
2016-07-03 13:28:27 cri

Hukumar hasashen yanayi ta lardin Hunan dake kudu maso tsakiyar kasar Sin ta yi kashedi game da yiwuwar fuskantar ruwan sama mai tsanani, ta ce za a samu ruwan sama mai tsanani a yankin arewacin lardin.

Bisa kididdigar da ofishin bada umurni ga magancen ambaliyar ruwa na lardin Hunan ya yi, an ce, ya zuwa karfe 8 na daren ranar 2 ga wata, akwai mutane dubu 306 ne da bala'in ya shafa, kuma an kwashe mutane dubu 22 cikin gaggawa.

Yanzu ana kokarin yaki da bala'in a yankin, da tsugunar da mutanen da bala'in ya shafa, kuma hukumomi ciki har da hukumar kula da harkokin jama'a ta lardin, sun kai kayayyakin taimako zuwa yankin mai fama da bala'in. Bayan faruwar gangarowar duwatsu, gwamnatocin yankin sun yi kokarin bada ceto da tabbatar da tsaron mutane.

Bisa bayanin da hukumar kula da albarkatun ruwa ta lardin Hunan ta yi, an yi ruwan sama mai tsanani a arewa da kudu maso yammacin lardin tun daga ranar 1 ga wannan wata, wanda ya haddasa karuwar igiyar ruwan koguna dake lardin. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China