A yayin ganawar tasu, Mr. Wang ya ce, kasar Sin tana son ba da taimako ga kasar Saliyo kan aikin farfado da tattalin arziki da kyautata yanayin zamantakewar al'ummar kasar tun bayan kawo karshen yaduwar cutar Ebola a kasar, kana da kuma zurfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, bisa ka'idojin da aka cimma matsaya guda kansu a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC da aka gudanar a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. (Maryam)