Tawagar kwararrun likitoci na Najeriya da takwarorinsu na kasar Indiya ne suka gudanar da aikin tiyatar zuciya ga wasu yara kanana su 6 da kuma wani babban mutum guda.
Babban daraktan asibitin na LUTH Chris Bode, ya tabbatar wa manema labarai a birnin Legas, cewa an gudanar da aikin tiyatar zuciyar ce cikin makonnin da suka gabata tun bayan kafa sashen tiyatar zuciya a asibitin koyarwa na jami'ar ta Legas a shekarar 2014 tare da hadin gwiwar shirin inshorar lafiya ta kasar.
Ya kara da cewar, cibiyar ta kuduri aniyar aiwatar da aikin tiyatar zuciyar kimanin 100 nan da shekarar 2017.
Bode yace wannan nasarar da aka samu babban abin alfahari ne ga fannin kiwon lafiya na kasar, kuma zai takaita yawan fita zuwa kasashen ketare da 'yan kasar suke yi domin neman magani.