in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na fatan ba da gudummawa wajen bunkasa fannin kiwon lafiya na shekarar 2030
2016-05-24 09:41:44 cri

A jiya Litinin, darektar kwamitin kiwon lafiya da kayyade iyali na kasar Sin Li Bin, ta bayyana cewa gwamnatin kasar Sin na goyon bayan kudurin hukumar lafiya ta duniya WHO, game da nufin ta na tabbatar da burin neman samun dawaumammen ci gaba a fannin kiwon lafiya nan da shekarar 2030 a dukkanin fadin duniya, da mataki na shiyya-shiyya.

Madam Li Bin wadda ta bayyana hakan cikin jawabita ga taron muhawara na kiwon lafiya na duniya karo na 69, ta jaddada cewa kasar Sin na fuskantar kalubale a fannonin karuwar yawan tsoffi, da rashin daidaito wajen bunkasa aikin kiwon lafiya, da kuma rashin tsarin ba da tabbaci a fannin kiwon lafiya mai inganci.

Ta ce kana kasar ta Sin ba ita ce kadai ke fama da wadannan matsaloli ba, kasashe daban daban na duniya su ma suna fuskantar wadannan kalubale. Don haka Sin ke fatan kara bunkasa aikin kiwon lafiya, da zage damtse tare da sauran kasashe mambobin hukumar ta WHO, wajen tabbatar da burin neman samun dawaumammen ci gaba, wanda zai kara yawan gudummowa ga karfafa aikin kiwon lafiyar bil Adama, da tabbatar da dawaummamiyar bunkasuwa a duniya baki daya. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China