Clever Mafuta, darektan tsarin Transboundary Water wato ruwan kan iyakoki, da cibiyoyin MDD da dama suke amfani da shi, ya bayyana cewa lalacewar kasa, gurbacewar iska, rashin kyawawan tsare tsaren kiwon lafiya da gurbacewar ruwan sha na daga cikin matsalolin muhalli mafi kamari a nahiyar Afrika.
Kwararren na MDD ya bayyana cewa dogaron Afrika kan amfani da itacen girki, samar da haske da dumama gidaje zai janyo hadura ga lafiyar kashi 90 cikin 100 na al'ummar nahiyar sakamakon gubacewar iska, dake janyo mutuwar jarirai dubu dari shida a kowace shekara a Afrika. (Maman Ada)