in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da manyan jami'an kasar Amurka
2016-06-08 09:29:57 cri
Firaministan kasar Sin mista Li Keqiang, ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, da sakataren baitulmalin kasar Jacob Lew, a babban dakin taron jama'ar kasar Sin da ke nan birnin Beijing a ranar Talata.

Manyan jami'an 2 daga bangaren kasar Amurka sun iso kasar Sin ne don halartar shawarwarin bangarorin 2, ta fuskar manyan tsare-tsare, da tattalin arziki a karo na 8, gami da taron musayar ra'ayi tsakanin manyan kusoshin bangarorin 2 a fannin al'adu a karo na 7.

Yayin ganawarsu, firaminista Li Keqiang ya ce, huldar dake tsakanin bangarorin Sin da Amurka na samun karin ci gaba, inda moriyar bai daya dake tsakaninsu ta fi bambancin ra'ayin su yawa. Don haka kasar ta Sin ke fatan ci gaba da mu'amala tare da Amurka, musamman ma a tsakanin shugabannin su, tare da kokarin karfafa amincewa juna tsakanin su, da habaka hadin gwiwar su, da daidaita bambancin ra'ayinsu yadda ya kamata, don kara kyautata huldar dake tsakanin kasashen 2.

Firaministan ya kara da cewa, Sin na fatan zurfafa hadin kai ta fannin tattalin arziki da cinikayya tare da kasar Amurka, da kula da moriyar ko wane bangare, da ci gaba da kokarin musayar ra'ayi tsakaninsu, don tabbatar da cimma burin kulla ingantacciyar yarjejeniyar zuba jari, wadda za ta amfani dukkan bangarorin 2.

Haka zalika, firaministan kasar Sin ya kara da cewa, Sin na fatan kara musayar ra'ayi tare da bangaren Amurka, dangane da batun karfafa hadin gwiwar da ake yi tsakanin mambobin kungiyar G20, tare da tabbatar da ganin taron koli na kungiyar da zai gudana a birnin Hangzhou na kasar Sin ya samar da sakamako mai kyau.

A nasu bangare, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry, da sakataren baitulmalin Amurka Jacob Lew, sun bayyana cewa, musayar ra'ayin da ake yi a wannan karo tana tare da nasarori masu yawa. Hakan, a cewarsu, ya nuna cewa, matakan na taimakawa zurfafa fahimtar juna, da hadin kai tsakanin bangarorin 2, da ma bunkasa yunkurinsu na shawo kan bambancin ra'ayi.

Har wa yau a cewar su, kasar Amurka tana yaba wa kasar ta Sin, kan yadda ta tsaya kan manufar gyare-gyare da bude kofa, da rage samar da wasu kayayyakin masana'antun da ba sa bukata. Jami'an na Amurka na kuma fatan za a kara azama ga shawarwarin da ake yi ta fuskar aikin zuba jari, gami da karfafa hadin gwiwar da take yi tare da kasar Sin, karkashin inuwar tsarin kungiyar G20. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China