Gwamnatin Sin ta dauki niyyar gina wannan ginin kiwon lafiya ga kasar Saliyo bisa dalilin cewa wannan kasa ta yi fama da annobar Ebola, da kuma halin shirye shiryen kasar na kyautata tsarin kiwon lafiyarta, in ji Gao Fu, mataimakin darektan cibiyar sa ido da rigakafi kan cututtuka ta kasar Sin, bayan ya samu ganawa tare da shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma a ranar Talata a fadar shugaban kasa.
Mista Fu ya shaidawa manema labaru bayan wannan ganawa, cewa ya samu tattaunawa mai fa'ida tare da shugaba Koroma, da ya nuna godiya kan taimakon da kasar Sin take baiwa kasarsa a lokacin da ake cikin bukata.
Sin na daga cikin kasashe na farko da suka amsa kiran neman taimakon jin kai cikin gaggawa a lokacin annobar Ebola da ta daidaita kasashen Saliyo, Liberiya da Guinee.
Kasar Sin ta samar da taimako na Yuan miliyan 750 kimanin dalar Amurka miliyan 113.77 da kuma tura dubban ma'aikatan kiwon lafiya zuwa kasashen da suka yi fama da annobar tun farkon shekarar 2014. (Maman Ada)