A yayin bikin, Mr. Oberer ya ce, ya mika lambar yabo din ga tawagar likitanci ta Sin a madadin gwamnatin kasar Kamaru, domin nuna mata yabo kan babban taimakon da ta samar wa asibitin Mbalmayo, haka kuma, ya yi godiya ga gwamnatin kasar Sin kan taimakon da Sin ta baiwa kasar Kamaru a fannin likitanci, da kuma babban gudummawa da kasar Sin ta bayar wajen kyautata yanayin kiwon lafiyar al'ummomin birnin, haka kuma, al'ummominsa za su ci gaba da nuna godiya kan taimakon da suka samu a ko da yaushe. (Maryam)