Rahoton ya tabo batun manyan shirye-shiryen hadin gwiwa 10 dake tsakanin Sin da Afirka, inda ya bayyana cewa, ko da ana samun yanayi maras kyau wajen raya tattalin arzikin duniya a halin yanzu, amma kasar Sin ta jaddada cewa, za ta ci gaba da taimakawa kasashen Afrika wajen aiwatar da muhimman ayyuka, kuma babban burin kasar Sin wajen fitar da manyan harkokin hadin gwiwar 10 a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da Afirka da aka yi a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a watan Disambar shekarar 2015 shi ne, domin taimakawa kasashen Afirka wajen kawar da talauci, da kuma cin moriyar juna.
Bugu da kari, rahoton ya bayyana cewa, bayan da aka kammala taron, ba tare da bata lokaci ba, kasar Sin ta fara yin shawarwari tare da kasashen Afirka da abin ya shafa, domin aiwatar da shirin yadda ya kamata. (Maryam)