Makasudin shirya taron mai taken "Saka jari a kasar Kamaru, kasa mai dama", shi ne a baiwa masu saka jari na kasashen waje damar raya tattalin arziki da Kamaru take da shi, gami da damar saka jari.
A jawabinsa yayin bikin bude taron, shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya bayyana cewa, Kamaru na da fiffiko a wasu fannoni da dama wadanda za a saka jari a ckinsu, baya ga albarkar kasa mai kyau, da albarkatun ma'adinai, da yanayi, da yankunan kasa, kuma dukkan wadannan suna taimakawa aikin gona a wurin. Ban da wannan kuma, tashar jiragen ruwa, da filin jiragen sama, da hanyoyin jiragen kasa da na mota da sauran muhimman ababen more rayuwa sun taimakawa aikin raya yankunan da ciniki tsakanin kasa da kasa.
Wakilan kasashen duniya sama da 500 ne suka halarci taron da za a shafe kwanaki 2 ana yinsa, inda tsohon shugaban hukumar zartarwar kungiyar EU José Manuel Durão Barroso da tsohon firaministan kasar Koriya ta Kudu CHUNG UN-CHAN sun yi jawabi a yayin bikin bude taron.(Bako)