Tare da rakiyar mambobin gwamnatinsa da ba'a bayyana sunanyensu ba da farko da kuma matarsa Chantal, shugaban kasar Kamaru ya bar birnin Yaounde kafin misalin karfe goma na safe bisa agogon wurin zuwa babban birnin Najeriya, inda ya samu babban tarbo daga takwaransa Muhammadu Buhari.
Wannan shi ne karo na biyu da shugabannin kasashen biyu suke ganawa a tsawon kusan shekara daya bayan ganarwarsu ta farko a yayin ziyarar shugaba Buhari a birnin Yaounde a ranakun 29 da 30 ga watan Yulin shekarar 2015, watanni biyu bayan kama aiki a matsayin sabon shugaban Najeriya, kasa ta farko a fuskar tattalin arziki a yammacin Afrika bayan nasarar kan shugaba mai barin gado Goodluck Jonathan a zaben shugaban kasa na ranar 29 ga watan Maris. (Maman Ada)