Koda yake sanarwar ba ta bayyana makasudin ziyarar ba, amma ana ganin cewa musanyar tsakanin shugabannin biyu za ta mai da hankali kan yaki da kungiyar Boko Haram da kasashen biyu suke gudanarwa a cikin rundunar hadin gwiwa da kwamitin tafkin Chadi (CBLT) ya kafa da kuma kasashen biyu suke mamba.
A cikin watan Yulin shekarar 2015, kimanin watanni biyu bayan rantsar da shi a karshen watan Mayu a birnin Abuja, mista Buhari ya kai irin wannan ziyarar aiki a birnin Yaounde tare da wannnan muhimmin batun yaki da Boko Haram. Tun lokacin, Yaounde da Abuja suka karfafa dangantaka, musammun ma a fannin yaki da ta'addanci. (Maman Ada)