in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron ministoci karo na 7 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa a birnin Doha
2016-05-13 11:01:15 cri
A jiya Alhamis 12 ga wata, ministan harkokin waje na Sin Wang Yi, da takwaransa na Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al-Thani, da kuma babban sakataren kungiyar tarayyar kasashen Larabawa Nabil Elaraby sun halarci bikin rufe taron ministoci karo na 7 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Larabawa.

Minista Wang Yi ya bayyana cewa, taron ministocin ya samu babbar nasara, kuma wani muhimmin taro ne da ya hada baya da gaba, inda aka zurfafa ra'ayin hadin gwiwa, da raya dankon zumunci tsakanin Sin da kasashen Larabawa, da karfafa hakikanin hadin gwiwa tsakaninsu, domin sa kaimi ga bunkasa dangantaka tsakanin Sin da kasashen Larawaba da ta zama abin koyi a fannin hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa a duniya.

Kasashen Larabawa sun amince da babban sakamakon da aka samu, kuma suna ganin cewa, takardun da aka zartas da su a gun taron sun bayyana ra'ayoyin bangarorin biyu, tare da yin fasali kan muhimman fannnonin da za su yi hadin gwiwa a kai a nan gaba, ta yadda za a sa sabon kuzari ga bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen Larabawa da Sin.

A gun taron kuma, an zartas da kuma rattaba hannu kan sanarwar Doha da shirin matakan da za a dauka daga shekarar 2016 zuwa ta 2018.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China