in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Larabawa sun nuna goyon baya game da cikakken yanki da mulkin kai na kasar Sin
2016-05-13 10:26:09 cri
A ranar 12 ga wata, bayan da sakatare janar na kungiyar hadin gwiwa kan kasashen Larabawa Nabil Elaraby ya halarci taron ministoci karo na 7 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa, inda kuma ya halarci taron manema labaru tare da ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, da ministan harkokin wajen Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman bin Jassim Al-Thani.

Elaraby ya ce, bayan da aka kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwar Sin da kasashen Larabawa, an samu sakamako mai gamsarwa. An shirya taro na wannan karo cikin nasara, abun da ya nuna dankon zumunci dake tsakanin kasashen Larabawa da Sin da babbar anniyar samun ci gaba tare na bangarorin biyu. Sin ta samu babban ci gaba a cikin 'yan shekarun nan, akwai fasahohin zamani da dama da Sin za ta iya taimakawa kasashen Larabawa, kasashen Larabawa za su inganta hadin gwiwa da kasar Sin wajen aiwatar da manufar Ziri Daya da Hanya Daya.

Elaraby ya ce, kasashen Larabawa sun nuna goyon baya game da cikakken yanki da mulkin kai na kasar, kuma sun nuna goyon baya game da matsayin da Sin na tsayawa karkashin inuwar yarjejeniyar kiyaye teku ta M.D.D..An bayyana hakan cikin sanarwar Doha da aka fidda a wannan rana, kasashen Larabawa da Sin za su ci gaba da nuna wa juna goyon baya game da manyan batutuwan dake shafar ko wanensu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China