in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Membobin kungiyar kasashen Larabawa sun amince da kafa hadaddiyar rundunar soja.
2015-03-30 10:49:11 cri

A lahadin nan aka rufe taron koli na kungiyar kasashen Larabawa AL karo na 26 a birnin Sharm El-Sheikh dake gabar kogin Bahar Maliya na kasar Masar, inda shugaban kasar Abdel-Fattah El-Sisi ya bayyana cewa, membobin kungiyar kasashen Larabawa sun amince da kafa hadaddiyar rundunar soja bisa wasu ka'idoji domin tinkarar kalubalen tsaro.

Abdel-Fattah El-Sisi ya kara da cewa, hadaddiyar rundunar za ta dauki matakan soja a wasu kasashe membobi bisa bukatunsu a yayin da suke fuskantar kalubale da kuma barazana a fannonin tsaron yankin kasa da mulkin kai.

Bisa sanarwar da aka bayar a gun taron, kasashe membobin kungiyar za su shiga hadaddiyar rundunar soja bisa sonsu, kuma an ba da labarin cewa, wannan hadaddiyar rundunar soja za ta kunshi sojoji dubu 40, sannan watakila za a samar da jiragen sama da jiragen ruwa na soja da kuma motoci masu sulke.

Ministan harkokin waje na kasar Masar Sameh Shoukry ya ce, in aka kafa hadaddiyar rundunar soja, za ta kasance kamar dawamammiyar runduna. Yana mai bayanin cewa, shugabannin kasashen Larabawa za su ci gaba da tuntubar juna kan ayyukan kafa rundunar soja da hanyoyin daidaita rikici da kuma sauransu, kuma za su fitar da sakamako a cikin watanni 4 masu zuwa.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China