in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Chadi ya gana da wakilin majalisar gudanarwa ta Sin
2016-05-08 13:02:15 cri
Jiya Asabar 7 ga wata, shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya gana da wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin Yang Jiechi a babban birnin kasar Chadi, Ndjamena.

A yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya bayyana cewa, cikin shekarar da ta gabata, sau biyu shugaban kasar Sin Xi Jiping da shugaba Deby suka yi ganawa, inda suka tabbatar da kyakkyawar makomar bunkasuwar dangantaka a tsakanin kasar Sin da kasar Chadi. A halin yanzu, ana gamuwa da sabbin damamankin habaka hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, shi ya sa, kasar Sin tana son aiwatar da harkokin da shugabannin kasashen biyu suka tsara yadda ya kamata, yayin da kuma ake karfafa fahimtar siyasa a tsakanin Sin da Chadi. Haka kuma, ana fatan karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin aikin gona, gina ababen more rayuwa, da kawar da talauci da dai sauransu, a yayin da ake gudanar da sakamakon dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, ta yadda za a iya sa kaimi ga kamfanonin kasar Sin da su kara zuba jari a kasar Chadi, da kuma taimaka wa kasar wajen neman bunkasuwar tattalin arziki da zaman takewar al'umma.

A nasa bangare kuma, shugaba Deby ya ce, kasar Sin tana goyon bayan kasashen Afirka wajen yin hadin gwiwa da neman bunkasuwa ko da yaushe, ita ce abokiyar arziki ta kasar Chadi da ta al'ummomin kasashen Afirka baki daya. An kuma cimma sakamako masu kyau da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Chadi da kuma a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wadanda suka burge al'ummomin kasashen Sin da Afirka matuka.

Game da haka, kasar Chadi ta gamsu sosai dangane da bunkasuwar dangantaka a tsakanin kasashen biyu, tana kuma matukar godiya ga kasar Sin bisa taimakon da ta samar wa kasar wajen raya tattalin arzikinta, tana kuma maraba da zuwan kamfanonin kasar Sin a Chadi, ta yadda za a iya ci gaba da inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa fannoni daban daban kuma yadda ya kamata.

A wannan rana kuma, Yang Jiechi ya gana da firaministan kasar Chadi Albert Pahimi Padacke, inda suka cimma ra'ayi daya cewa, an sami sakamako da dama bisa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, a nan gaba kuma, ana son ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Chadi a fannonin sufuri, wutar lantarki, masana'antu, aikin ban ruwa, ayyukan noma da kiwon dabbobi da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China