Tsohun faraminista, Joseph Djimrangar Dadnadji, wanda ya koma adawa ya samu kashi 5 cikin 100 na kuri'un da aka jefa.
A ranar 10 ga watan Afrilu, kashi 76.11 cikin 100, kimanin miliyan 6.2 na 'yan Chadi da suka yi rijistan zabe sun fito domin zaben sabon shugaban kasa. A ranar Laraba, 'yan takara takwas sun yi barazanar kafa wata "gwamnatin ceton kasa" idan har hukumar zabe ta sanar da shugaba mai ci a matsayin wanda ya lashe zabe.
Haka kuma sun yi kashedi ga hukumar zabe da kwamitin tsarin mulki kan duk wani yunkurin tabbatar da wannan satar zabe, tare da niyyarsu ta kin amincewa da hukumomin da za su biyo bayan wannan satar zabe, idan ba su samu biyan bukatunsu ba za su kafa wata gwamnatin ceton kasa domin amsa bukatun 'yan kasar Chadi, in ji sanarwar wadannan 'yan takara takwas. (Maman Ada)