Kwamitin tsarin mulkin kasar Chadi, ya sanar da sakamakon karshe na zaben shugaban kasar a jiya Talata, sakamakon da ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar Patriotic Salvation Movement mai mulkin kasar, kuma shugaban kasar mai ci Idriss Déby ne ya lashe babban zaben kasar.
Kwamitin tsarin mulkin kasar ta Chadi ya sanar a wannan rana cewa, a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 10 ga watan Afrilu, shugaban Déby ya samu kuri'u da yawansu ya kai kashi 59.92 dari, kuri'un da yawansu ya zarce rabin jimillar da aka kada, don haka zai zarce a matsayin shugaban kasar. (Zainab)