in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara jefa kuri'ar babban zaben kasar Chadi
2016-04-10 18:15:28 cri
An bude rumfunan zabe a wurare daban daban na kasar Chadi a safiyar ranar Lahadi don fara aikin jefa kuri'a a zagayen farko na babban zaben kasar.

Ana sa ran ganin jama'ar kasar fiye da miliyan 6.2 wadanda suke cikin kasar ko kuma a ketare, zasu kada kuri'a domin zaben daya daga cikin 'yan takara 14 dake neman kujerar shugabancin kasar.

Shugaban kasar mai ci Idriss Deby Itno ya kwashe shekaru 25 yana mulkin wannan kasa dake yammacin Afrika, sa'an nan a wannan karo zai nemi samun wa'adin aikinsa na 5.

Sauran abokan hamayyar shugaba Deby sun hada da shugaban 'yan adawa Saleh Kebzabo da tsohon firaminista Joseph Djimrangar Dadnadji.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China