A sakon da ya aiko ma takwaransa Shugaba Xi Jinping,a ranar talatan nan 1 ga watan oktoba,Mr Deby ya jinjina ma kyakkyawan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu tare da fatan inganta shi zuwa sabon matsayi nan gaba domin amfanawa al'ummomin kasashen.
Ya ce huldar dake tsakanin Sin da Chadi da aka farfado da shi shekaru 6 da suka gabata ya zama abin koyi a bayyane. (Fatimah Jibril)