in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan adawar kasar Chadi sun yi watsi da nasarar shugaban kasa mai ci ya samu
2016-04-23 12:15:13 cri
Wasu 'yan takarar zaben shugaban kasar Chadi na ranar 10 ga watan Afrilun da ya gabata a kasar Chadi sun jaddada a ranar Jumma'a da kin amincewarsu da nasarar shugaban kasa mai ci wato Idriss Deby Itno, da sakamakon wucin gadi ya nuna shi ya lashe zaben. A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, Laoukein Kourayo Medard, Joseph Djimrangar Dadnadji, Gali Ngothe Gatta, Saleh Kebzabo, Mahamat Ahmat Alhabo da kuma Brice Mbaimon Guedmbaye sun yi allawadai da "satar zabe" tare da yin kira ga al'ummar kasa da su tashi tsaye domin kare tsarin demokaradiyya da kuma kare 'yancin kasa. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China