in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi zaben shugaban kasa a Chadi
2016-04-11 10:09:25 cri
An kada kuri'u a babban zaben shugaban kasar Chadi a ran 10 ga wata, inda 'yan takara guda 13, ciki hada da dan takarar jam'iyyar mai mulkin kasa a halin yanzu, watau jam'iyyar tabbatar da kishin kasa ta Idriss Deby suka shiga wannan babban zabe.

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ta fidda labarin cewa, adadin masu jefa kuri'u da suka yi rajista ya kai miliyan 6, wadanda suka kada kuri'u a rumfunan zabe dake wurare daban daban a wannan rana. Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa, za a gabatar da sakamakon zaben bayan makwanni biyu, kana, idan babu wanda ya samun kuri'u na kashi 50 bisa dari, za a je zaben shugaban kasar zagaye na biyu.

Idriss Deby ya kafa jam'iyyar tabbatar da kishin kasa a watan Maris na shekarar 1990, ya kuma kasance shugaban jam'iyyar, sa'an nan, a watan Disamba na shekarar 1990 ya hau kujerar shugaban kwamitin harkokin kasar Chadi. Daga bisani kuma, a watan Maris na shekarar 1991, ya zama shugaban kasar Chadi, inda ya kuma ci gaba da lashe babban zaben shugaban kasar har sau duhu a shekara ta 1996, 2001, 2006 da kuma shekarar 2011. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China