Wannan abon kamfanin simintin na yankin Ngara dake kudu maso yammacin kasar, wanda zai rika samar da ton dubu biyar a shekara ta farko, daga bisani kuma za'a iya samar ton miliyan guda a kowace shekara.
Ayyukan gina wannan masana'anta, an mika su ga wani kamfanin kasar Sin, kuma za su kwashe watanni goma sha biyu bisa jimillar kudin Sefa biliyan 30 kimanin dalar Amurka miliyan 60.
Sabon kamfanin simintin zai zo ya karfafa aikin kamfanin farko da ya fara aiki a Baore, duk a yanki guda da ke kan iyaka da kasar Kamaru. Wanda kamfanin kasar Sin na CAMCE ya gina bisa wani rancen kudi daga bankin Eximbank na kasar Sin, kamfanin simintin Baore na samar da ton dubu dari biyu a kowace shekara, abin da ya yi kasa sosai da bukatun dake ci gaba da karuwa da fiye da ton dubu dari bakwai a kowace shekara a cikin kasar da ke ci gaba da samun sauyi sosai. (Maman Ada)