Cikin sanarwar, an bayyana cewa, kwamitin sulhu na MDD yana maraba da kwamitin da firaministan kasar Libya ya fara aiwatar ba tare da bata lokaci ba, domin warware matsalolin dake shafar harkokin siyasa, da tsaro, da jin kai, da tattalin arziki da kuma batun hukumomin kasar da dai sauransu, ta yadda za a iya tunkarar kalubalen ta'addanci, sannan ya yi kira ga bangarori daban daban na kasar da abin ya shafa, da su nuna goyon baya domin cimma wannan buri.
Kwamitin sulhu na MDD ya yi kira ga dukkanin al'ummomin kasar Libya da su aiwatar da yarjejeniyar siyasar kasar cikin kwanciyar hankali, da nuna fahimtar juna yadda ya kamata, domin kada a haifar da illa ga matakan sauyin siyasa a kasar.
Bugu da kari, kwamitin ya nuna damuwarsa matuka kan kalubalen ta'addanci da kasar take fuskanta a halin yanzu, inda ya kuma yi kira ga gwamnatin hadin gwiwar al'ummomin kasar da ta mai da hankali yadda ya kamata wajen tunkarar kalubalen. (Maryam)