Wani jami'in soji na kasar Libya ya fadawa wakilinmu cewa, bayan rangama a tsakanin bangarrin biyu, sojojin kasar sun mamaye tashar ruwa ta Marisa ta birnin Banghazi da sauran yankunan da dakarun suka mamaye, kuma sun kashe dakaru a kalla 15, su ma sojoji a kalla 3 suka rasa rayukwan su a lokacin fadar.
Wannan jami'i ya ce, tashar ruwa ta Marisa tana da muhimmancin gaske, idan aka mamaye wannan tasha, za a katse mu'amalar mutane da kayayyaki tsakanin dakarun dake yankunan gabashi da na yammacin kasar.
A wata sabuwa kuma, sojojin kasar sun mamaye birnin Ejdabia da ke da nisan kilomita 150 a kudu da birnin Banghazi. Wani likita na asibitin wurin ya ce, a cikin watanni biyu da suka gabata, mutane 65 sun mutu sakamakon rikici, tare da raunatar wasu 140.
Bayan da aka kawo karshen gwamnatin Gaddafi a shekarar 2011, kasar ta shiga tangal-tangal. A watan Agustan shekarar 2014, aka samu majalisun dokoki guda 2 da gwamnatoci guda 2 da suke fito-na-fito da juna, lamarin da ya haifar da artabu tsakanin dakaru masu dauke da makamai na bangarorin biyun, hakan ya baiwa kungiyar 'yan ta'adda da kungiya masu tsattsauran ra'ayi damar kara karfinsu a kasar. Yanzu, kungiyar IS ta mamaye birnin Sirte da Derna da ke yankin gabashin kasar, kuma sun kafa rassansu a birane Tripoli da Banghazi.(Bako)