Firaministan kasar tsagin gwamnatin dake ikirarin mulkin birnin, Khalifa Ghwel, ya ce za su zartas da wannan doka ne a dukkanin fadin kasar, yayin da kuma majalissar zartaswar kasar za ta ci gaba da gudanar da zama na dindindin. Mr. Ghwel, ya kara da cewa ya umarci sassan jami'an tsaro da su shiga damarar tabbatar da tsaro, da kuma sintiri kan iyakokin kasa.
A nasa bangare firaministan gwamnatin dake samun goyon bayan MDD, wadda kuma ke da helkwata a birnin Tunis, Feyez Serraj, ya ce suna nan kan bakan su, na maida harkokin gwamnatin su zuwa birnin na Tripoli nan da 'yan kwanaki masu zuwa, suna kuma da cikakken goyon baya daga sassan jami'an tsaro ciki hadda sojojin kasar.
Gwamnatin hadin gwiwa da Mr. Serraj ke jagoranta dai ta kafu ne, bayan amincewa da ta samu daga bangarorin wasu jam'iyyun siyasar kasar masu adawa da juna. Sai dai tsagin gwamnatin dake rike da ikon birnin Tripoli ya yi fatali da wannan mataki. Kaza lika ya zuwa yanzu, sassan biyu na gudanar da gwamnatoci biyu masu nuna yatsa ga juna.(Saminu Alhassan)